Aiki ga mai kareka: Babban sufetan Yansanda ye nemi izinin yin binciken kwakwaf akan Lawal Daura

Aiki ga mai kareka: Babban sufetan Yansanda ye nemi izinin yin binciken kwakwaf akan Lawal Daura

Babban sufetan Yansandan Najeriya, IG Ibrahim Idris ya nemi izinin mukaddashin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo don gudanar da bincike a gidan tsohon shugaban hukumar DSS, Lawal Daura don gano wasu muhimman takardu.

Legit.ng ta ruwaito babban sufetan Yansandan na tabbatar ma Osinbaje cewa Lawal na tsare a wani gida, sa’annan yace jami’an Yansandan dake bincikarsa sun samu muhimman bayanai daga gareshi.

KU KARANTA: Babu abin da ka tabuka game da cigabanmu – Matasan jihar Sakkwato ga Tambuwal

Aiki ga mai kareka: Babban sufetan Yansanda ye nemi izinin yin binciken kwakwaf akan Lawal Daura

Lawal Daura

A ranar Talatar data gabata ne dai Osinbajo ya sallami Lawal daga aiki biyo bayan mamaye majalisar dokokin Najeriya da jami’an hukumar DSS suka yi inda suka hana yan majalisu shiga majalisar ba tare da izinin fadar shugaban kasa ba, kuma tuni aka maye gurbinsa da Mathew Seyeifa dan asalin jihar Bayelsa.

IG ya bayyana bukatar bincikar gidan lawal ne cikin rahoton da ya mika ma mukadashin shugaban kasar bayan Yansanda sun yi ma Lawal tambayoyi bisa bahallatsar da ta faru a majalisar, inda yace sun fahimci wasu manyan yan siyasa ne suka daure masa gindi.

Da wannan ne IG Idris ke neman sahhalewar Osinbajo don aikawa da kwararrun jami’an Yansanda zuwa gidan Lawal Daura su binciko duk wasu muhimman takardun ko kuma bayanai da zasu taimaka musu wajen binciken da suke yi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel