Dalilin da zai hana Saraki murabus - Bafarawa

Dalilin da zai hana Saraki murabus - Bafarawa

Tsohon gwamnan jihar Sakkwato kuma daya daga cikin manema tikitin takarar kujerar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Alhaji Attahiru Bafarawa, ya bayyana dalilin sa na cewar shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki ba zai iya barin mukamin sa ba.

Kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito, tsohon gwamnan ya bayyana cewa, Saraki ba zai iya barin kujerar sa ba sakamakon aikata hakan zai sabawa tsarin dimokuradiyya a tarihin kasar nan.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne Bafarawa ya bayyana hakan cikin babban birnin kasar nan na Abuja, yayin ganawa da manema labarai a matsayin wani ɓangare na yakin neman zabe domin samun nasarar lashe tikitin takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019.

Dalilin da zai hana Saraki murabus - Bafarawa

Dalilin da zai hana Saraki murabus - Bafarawa
Source: Depositphotos

Yake cewa manufarsa muddin ya zamto shugaban kasar nan ba ta wuci tabbatar da tsaren-tsaren jam'iyyar sa ta PDP da kuma dabbakawa tare da tafiya kan kundin tsarin mulki na Najeriya.

Da yake ci gaba da tabbatar da dalilin sa Bafarawa ya bayyana cewa, a yayin da gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ke rike da kujerar kakakin majalisar wakilai, bai yi murabus ba bayan da ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC.

KARANTA KUMA: Jega ya yi kira a ƙaddamar da tsauraran dokoki kan shaci faɗin sakamakon Zaɓe

A sanadiyar haka tsohon gwamnan yake cewa, aikata hakan ga Saraki zai sabawa tsarin diomkuradiyya a tarihin kasar nan.

Legit.ng ta fahimci cewa, Bafarawa ya bayyana takaicin sa dangane da mamayar da jami'an tsaro na hukumar DSS suka kai harabar majalisar dokoki ta tarayya a da a cewar sa wannan babban abin kunya gami da tozarci a idon duniya ta fuskar zagon kasa ga dimokuradiyya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel