'Yan Boko Haram sun kai hari Sansanin Dakarun Soji, sun kar Dakaru 17 sun raunata 14 a jihar Borno

'Yan Boko Haram sun kai hari Sansanin Dakarun Soji, sun kar Dakaru 17 sun raunata 14 a jihar Borno

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ta wallafa da sanadin kalacen rahoton daga kafar watsa labarai ta AFP a ranar Alhamis din da ta gabata ta bayyana cewa, 'yan ta'adda na Boko Haram sun kai wani sabon hari sansanin dakaru da ya salwantar da rayukan soji 17 a jihar Borno.

Wannan shine hari na uku da 'yan ta'addan suka zartar cikin sansanai daban-daban na dakarun cikin abinda bai wuci wata guda ba a birnin na Maiduguri da ya zamto wata farfajiya ta'addanci tun shekaru 9 da suka gabata.

Rahotanni sun bayyana cewa, wani sabon hari ya auku ne yayin da masu jihadin rike da muggan makamai cikin motocin su na daukan kaya suka dirfafi sansanin dakarun sojin dake kauyen Garunda na jihar Borno a ranar Larabar da ta gabata.

Legit.ng ta fahimci cewa, aukuwar wannan hari na daya daga cikin munana na kwana-kwanan da 'yan Boko Haram suka zartar a sansanan dakarun soji dake Najeriya, da hakan ke ci gaba da barazana ga addinin Islama a yankin gami da haskaka gwamnatin kasar sakamakon ikirarin ta na cewar ta nakasta 'yan ta'addan tare da rusa su.

'Yan Boko Haram sun kai hari Barikin Soji, sun kar Dakaru 17 a jihar Borno

'Yan Boko Haram sun kai hari Barikin Soji, sun kar Dakaru 17 a jihar Borno

Kamar yadda wani dakarun soji ya shaidawa kafar watsa labarai ta AFP kuma ya bukaci a sakaya sunan sa ya bayyana cewa, 'yan ta'addan sun hallaka dakarun soji 17 tare da raunata 14 yayin aukuwar harin.

Dakarun sojin ya ci gaba da cewa, baya ga wannan mugun lahani da 'yan ta'addan suka yi a sansanin sun kuma arce motocin da kuma makamai da dama.

A ranakun 14 da 26 ga watan Yulin da ya gabata ne 'yan ta'addan suka kai makamancin wannan munanan hare-hare a sansanan dakarun soji dake kauyen Jilli na jihar Yobe da kuma wajen garin Maiduguri dake yakin Arewa maso Gabashin kasar nan.

KARANTA KUMA: Majalisar Tarayya za ta amince da kasafin kudin zaben 2019 a mako mai zuwa - Yakubu

Aukuwar wannan munanan hare-hare ta salwantar da rayukan dakarun soji da dama tare da muguwar ɓarna marar misali.

A yayin tabbatar da wannan lamari, hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa watau NEMA ta bayyana cewa, rayuwar wani ma'aikacin ta guda ta salwanta yayin da yake gudanar da wasu aikace-aikace a sansanin dakarun sojin dake garin Damasak na jihar Borno.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel