Canji: Ma’aikatar gwamnatin tarayya ta mayar da biliyan N3bn aljihun gwamnati

Canji: Ma’aikatar gwamnatin tarayya ta mayar da biliyan N3bn aljihun gwamnati

Ma’aikatar ma’adanai dad a inganta karafa ta bayyana cewar ta zuba zunzurutun kudi da yawansu ya kia biliyan N3bn a asusun gwamnatin tarayya.

Karamin ministan ma’aikatar, Abubakar Bwari, ya sanar da haka a Ikeja ta jihar Legas yayin gabatar da jawabi a wani taro day a halarta.

Ya bayyana cewar adadin kudaden da ma’aikatar ke samarwa gwamnatin tarayya ya karu tun bayan hawan shugaba Buhari.

A cewar Bwari an samu karuwar kudaden shigar ne saboda wasu sabbin tsare-tsare da dokoki da gwamnatin shugaba ta gabatar bayan ta karbi ragamar gwamnatin tarayya a shekarar 2015.

Canji: Ma’aikatar gwamnatin tarayya ta mayar da biliyan N3bn aljihun gwamnati

Buhari da Ministoci

Kafin zuwan Buhari ma’aikatar na iya samar da miliyan N700m ne kawai amma yanzu abinda muka samar yah aura biliyan N3bn duk da an fuskanci zazzabin tattalin arziki na kusan shekaru biyu bayan zuwan wannan gwamnatin,” a cewar Bwari.

Bwari ya kara da cewar, “duk kasar dake bukatar harkar masana’antu tilas ta mayar da hankali wajen inganta harkar karafa. Hakan ya saka gwamnatin shugaba Buhari kirkiro sabbin manufofi da tsare-tsare da zasu inganta aiyukan ma’aikatar ma’adanai da karafa.”

DUBA WANNAN: Shugaba ya aiko da sakon yabo ga wasu dattijan arewa biyu

A bangaren irin kalubalen da ma’aikatar ke fuskanta, Bwari ya bayyana cewar babban kalubale da suke fuskanta shine na jigilar wasu karafa da ma’adanai tare da bayyana cewar suna bakin kokarinsu domin shawo kan matsalar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel