Mambobin APC 589,000 APC sun sanar da janyewarsu daga jam’iyyar a Edo

Mambobin APC 589,000 APC sun sanar da janyewarsu daga jam’iyyar a Edo

Guguwar sauya sheka da yayiwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), kawanya a fadin kasar ya isa mahaifar shugaban jam’iyyar Adams Oshiomhole, inda mambobin jam’iyyar sama da 589,000 suka sanar da janyewarsu daga jam’iyyar.

Masu sauya shekar da suka kasance mambobin kungiyar Kwankwasiyya a sabuwar APC a jihar Edo, sun samu jagorancin shugaban kungiyar na jihar, Cif John Osamede Adun da daraktan jam’iyyar na jihar, Hon Harrison Omagbon.

Lamarin na zuwa ne a lokacin da ake ta rade-radin cewa shugaban jam’iyyar na kasa kuma tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomhole zai je jihar domin sasanta gamayyar kungiyar jam’iyyar.

Mambobin APC 589,000 APC sun sanar da janyewarsu daga jam’iyyar a Edo

Mambobin APC 589,000 APC sun sanar da janyewarsu daga jam’iyyar a Edo
Source: Depositphotos

Da yake jawabi ga manema labarai a birnin Benin, Mista Omagbon yace sun yanke shawarar barin jam’iyyar ne bayan tattaunawa da kuma duba lamuran siyasar kasar.

KU KARANTA KUMA: Da wuya idan ba nine zan fara zama shugaban kasa a yan Igbo ba - Okorocha

Ya kuma bayyana cewa nan bada jimawa ba zasu san matakin gaba da zasu dauka bayan sun ji daga uban tafiyar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel