Yanzu Yanzu: Gwamna Okorocha ya sanar da hutun kwanaki biyu, tare da rufe kasuwa a Imo

Yanzu Yanzu: Gwamna Okorocha ya sanar da hutun kwanaki biyu, tare da rufe kasuwa a Imo

Gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo ya shawarci mazauna da mutanen jihar da su karbi katin zaben sun domin tabbatar da cewa an dama dasu a zabe mai zuwa.

Gwamnan ya kuma bayar da hutun kwanaki biyu domin ba mazauana yankin damar zuwa karban katin zaben su.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta rahoto cewa Okorocha, wanda ya bada shawarar a Owerri a ranar Alhamis, 9 ga watan Aguts yayin zantawa da manema labarai ya koka da rashin amsa kiran mazauna jihar Imo wajen zuwa karban katin zabe.

Yanzu Yanzu: Gwamna Okorocha ya sanar da hutun kwanaki biyu, tare da rufe kasuwa a Imo

Yanzu Yanzu: Gwamna Okorocha ya sanar da hutun kwanaki biyu, tare da rufe kasuwa a Imo

Gwamnan ya bayyana cewa jihar Imo ce keda mafi karancin wadanda suka yi rijista sannan kuma ita keda mafi karancin wadanda suka karbi katin a lokacin da aka kwatanta ta da sauran jihohin tarayyar kasar.

KU KARANTA KUMA: Majalisar dattawa bazata samu zaman lafiya ba har sai tsoffin gwamnoni sun daina mayar da ita gidan ritaya – Donald Duke

Don haka ya kaddamar da ranakun 15 da 16 ga watan Agusta a matsayin ranar hutu domin mazauna jihar su je su yi rijista sannan su karbi katinsu na zabe.

Sannan kuma gwamnan yayi umurni da a rufe kasuwanni a wannan ranaku domin tabbatar da goyon baya da sakamako mai kyau.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel