Jega ya yi kira a ƙaddamar da tsauraran dokoki kan shaci faɗin sakamakon Zaɓe

Jega ya yi kira a ƙaddamar da tsauraran dokoki kan shaci faɗin sakamakon Zaɓe

Mun samu rahoton cewa Farfesa Attahiru Jega, tsohon shugaban hukumar zabe watau INEC, ya yi kira ga gwamnatin tarayya akan ta ƙaddamar da tsauraran dokoki ga masu yada jita-jita ta sakamakon zaɓe na ƙarya gami da shaci faɗi.

Tsohon shugaban hukumar ya yi wannan kira cikin babban birnin kasar nan na Abuja a ranar Larabar da ta gabata yayin wani muhimmin taro da aka gudanar mai takie barazanar zantukan bogi da labarai na shaci faɗi ga 'yanci da kuma dimokuradiyyar kasar nan.

Yake cewa, lamarin labarai na karya ya zamto babbar barazana ga dimokuradiyyar kasar nan da ya kamata a shawo kansa cikin gaggawa.

Jega ya yi kira a ƙaddamar da tsauraran dokoki kan shaci faɗin sakamakon Zaɓe

Jega ya yi kira a ƙaddamar da tsauraran dokoki kan shaci faɗin sakamakon Zaɓe

Jega yake cewa, a yayin da zaben 2019 ke ci gaba da ƙaratowa akwai muhimmiyar buƙata ta ƙaddamar da tsauraran matakai da za su magance wannan lamari a ƙasar nan.

KARANTA KUMA: Jam'iyyu 6 na Siyasa sun sha alwashin tallafawa Matasan 'Yan Takara

Kamar yadda tsohon shugaban hukumar ya bayyana, akan yada labarai na karya da shaci fadi musamman a zaurukan sada zumunta ba tare da wasu hukunce-hukunce ko matakai.

A nasa bangaren, shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu ya bayyana cewa, a halin yanzu hukumar na fama da barzana ta yaduwar labarai na shaci fadi da ya kamata a fadakar da al'ummar kasar nan tare da wayar da kai ga illolin su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel