Da duminsa: Majalisa ta gimtse hutun ta, zasu dawo aiki sati mai zuwa

Da duminsa: Majalisa ta gimtse hutun ta, zasu dawo aiki sati mai zuwa

Mataimakin shugaban majalisar wakilai, Yussuf Lasun, ya sanar da cewar majalisar ta gimtse hutun da ta tafi tare da bayyana cewar zasu dawo bakin aiki ranar Talata ta sati mai kamawa.

Mista Lasun ya sanar da hakan ne ga manema labarai yau, Alhamis, a Abuja.

Kwanaki biyu da suka wuce ne wata kungiyar ‘yan majalisar wakilai (PDG) ta bayyana cewar ba zasu janye hutun da suka tafi ba matukar ana bukatar su dawo ne don a canja shugabancin majalisun tarayya ba.

Da duminsa: Majalisa ta gimtse hutun ta, zasu dawo aiki sati mai zuwa

Majalisa ta gimtse hutun ta, zasu dawo aiki sati mai zuwa

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar a Abuja ta hannun kakakinta, Honarabul Timothy Golu, ta bayyana cewar duk da shugabannin majalisar sun hadu domin tattauna yiwuwar dawowarsu bayan fadar shugaban kasa ta roke su, ‘yan majalisar sun bayyana cewar sai an yi masu alkawarin cewar ba za a taso da maganar canja shugabancin majalisun ba idan suka dawo.

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ya aiko da sakon yabo ga wasu dattijan arewa biyu

Ana saka ran majalisar zata tattuna tare da amincewa da sabon kasafin da shugaba Buhari ke bukatar su zartar.

Daga cikin karin kasafin da shugaba Buhari ke bukatar majalisun kasa su duba cikin gaggawa akwai batun amincewa da bawa hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) kudin da zata gudanar da zabukan shekarar 2019 da su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel