Sai wani ya mutu wani ke tashi: Sambo Dasuki na daf da fitowa bayan sauya sabon shugaban DSS

Sai wani ya mutu wani ke tashi: Sambo Dasuki na daf da fitowa bayan sauya sabon shugaban DSS

- Bayan sauyin da aka samu a hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) abubuwa na shirin faruwa

- Sabon shugaban hukumar na riko ya bayyana aniyarsa ta bincikar yadda ake tsare mutane ba bisa ka'ida ba

Da yiwuwar tsohon mai bawa shugaban kasa shawara Kanal Sambo Dasuki ya samu damar shekar iskar ‘yanci, biyo bayan tsige tsohon shugaban hukumar DSS Lawal Daura.

Sai wani ya mutu wani ke tashi: Sambo Dasuki na daf da fitowa bayan sauya sabon shugaban DSS

Sai wani ya mutu wani ke tashi: Sambo Dasuki na daf da fitowa bayan sauya sabon shugaban DSS

Sabon Daraktan riko na hukumar tsaro ta farin kaya ta DSS Mista Matthew Seiyefa ya shaida cewa zai bincika yadda ake tsare da tsohon mai baiwa tsohon shugaban kasar shawara da ya kai kimanin shekaru biyu a tsare.

KU KARANTA: Da duminsa: Jami’an EFCC sun kai mamaya gidan tsohon shugaban hukumar SSS

Matthew Seyifa ya bayyana hakan ne a yau a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Ofishinsa dake Abuja, inda ya shaida cewa hukumar zata bincika yadda ake tsare da sauran wadanda suke hannun hukumar.

Duk da cewa bai fadi ranar da za'a saki Sambo Dasukin ba, amma ya tabbatar da cewa za'a bincika yadda aka tsare shi din dama sauran wadanda hukumar ke tsare da su ba bisa doka ba. “An yi min bayanin yadda aka tsare Dasuki, amma zan bincika Iamarin sannu a hankali".

“Nan da wasu lokuta zamu binciki yadda al'amarin yake, musamman yadda hukumar tsaron farin kaya ta ke aikin hadin gwiwa tare da sauran hukumomin tsaro". Seyifa ya tabbatar.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel