Wani dan Najeriya ya yi bikin murnar cika shekaru 100 a gidan yari

Wani dan Najeriya ya yi bikin murnar cika shekaru 100 a gidan yari

Pa Celestine Egbunuche, dan Najeriya mafi tsufa a kurkuku ya yi bikin murnar cika shekaru 100 a duniya yayin da yake kulle a gidan yari na jihar Enugu.

Egbunuche, dan asalin Akokwa ta jihar Imo, ya yi murnar cika shekaru 100 din ne a ranar Asabar, 4 ga watan Agusta, 2018.

An yankewa Egbunuche tare da dan sa, Paul mai shekaru 87 a yanzu, hukunci bayan wani rikici a kan kasa da ya yi sanadin mutuwar wani mutum.

Wani dan Najeriya ya yi bikin murnar cika shekaru 100 a gidan yari

Wani dan Najeriya ya yi bikin murnar cika shekaru 100 a gidan yari

Yanzu haka Egbunuche da dan nasa sun shafe fiye da shekaru 17 a gidan yari. Sai dai wata kungiya mai zaman kanta na kokarin ganin sai an saki dattijon.

Kungiyar ta ce Egbunuche na fama da ciwon sukari na tsawon shekaru.

DUBA WANNAN: Yakin neman zaben APC: Osinbajo ya ziyarci sarkin Daura a fadar sa (Hotuna)

Kungiyar tayi kira ga gwamnan jihar imo, Rochas Okorocha, da ya saka baki domin a saki dattijon daga gidan yari.

Sau da dama kungiyoyi kan yi korafin yadda kotuna ke aike da jama'a gidan yari har a manta da su ba tare da an yanke masu hukunci ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel