Majalisar Tarayya za ta amince da kasafin kudin zaben 2019 a mako mai zuwa - Yakubu

Majalisar Tarayya za ta amince da kasafin kudin zaben 2019 a mako mai zuwa - Yakubu

Farfesa Yakubu Mahmoud, shugaban hukumar zabe na kasa watau INEC, ya yi karin haske dangane da wata muhimmiyar bukata ta shugaban kasa Muhammadu Buhari da majalisar dattawa take shirin cikawa nan ba da jimawa ba.

Shugaban hukumar ya bayyana cewa, akwai yiwuwar majalisar dokoki ta tarayyar kasar nan za ta bayar da sahalewar ta cikin mako ma gabatowa dangane da kasafin kudi na kumanin N242m domin gudanar da zaben 2019.

Mista Mahmoud ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai bayan ganawar sa da shugabannin majalisar cikin babban birnin kasar nan na tarayya a ranar Larabar da ta gabata.

Kamar yadda shafin jaridar Premium Times ya ruwaito shugaban na INEC ya bayyana cewa, majalisar tarayya kasar nan ta dauki kudiri dangane da dukufa domin tabbatar da gudanar da zaben 2019 cikin nagarta.

Majalisar Tarayya za ta amince da kasafin kudin zaben 2019 a mako mai zuwa - Yakubu

Majalisar Tarayya za ta amince da kasafin kudin zaben 2019 a mako mai zuwa - Yakubu

Legit.ng ta fahimci cewa, Farfesa yana kyautata tsammanin sa akan amincewar majalisar sakamakon gamsashiyar ganawa da ta gudana tsakanin sa da shugabannin ta, inda yake kyautata zaton samun amincin bukatar sa a mako mai gabatowa.

KARANTA KUMA: Kungiyar kasashen Turai, EU, ta bayyana damuwa kan mamayar da Hukumar DSS ta yiwa Majalisar Tarayya

Rahotannin sun bayyana cewa, a baya shugaba Buhari ya nemi majalisar akan ta gaggauta tanadin kasafin kudi na gudanar da zaben 2019, inda a halin yanzu ta fara gudanar da shirye-shiryen tabbatar da hakan.

Farfesa Yakubu ya kuma yabawa majalisar ta tarayya dangane da samun damar gudanar da wannan ganawa tsakanin sa da shugabannin ta, inda ya ce tuni hukumar sa ta kammala duk wani shiri na gudanar da zaben illa dai kudaden kaddamar da shirin take kirdado

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel