An saki Lawal Daura, amma an kwace masa fasfo

An saki Lawal Daura, amma an kwace masa fasfo

Jami’an hukumar leken asiri sun saki Babban Daraktan DSS Lawal Daura da aka dakatar bayan an kwace masa fasfo.

An sako shi ne a yammacin jiya Laraba, 8 ga watan Agust, daga gidan da ya ke a tsare, wanda jami’an SSS ne ke kula da shi, a Gwarimpa.

A can ya ke tsare tun lokacin da Osinbajo ya ba da umurnin sallamar shi daga aiki.

An bada umarnin a tsare shi bayan wasu zarge-zargen da aka ce ya aikata wasu laifuka da suka shafi cin amanar kasa da kuma kawo barazana ga tsaron kasa.

An saki Lawal Daura, amma an kwace masa fasfo

An saki Lawal Daura, amma an kwace masa fasfo

Da farko an bayar da rahoton cewa ya na tsare ne a Guzape, can a ofishin SARS a Abuja, inda ya dade ya na amsa wasu muhimman tambayoyi a hannun ‘yan sanda.

KU KARANTA KUMA: Wani ya hallaka abokinsa don kawai yayi soyayya da budurwarsa

Daga nan kuma an rika yawo da shi, daga wannan gida zuwa wancan a cikin Abuja. Daga nan an adana shi a wani gida da ke Gwarimpa.

A farkon makon nan ne dai mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinabajo ya dakatar da Lawal Daura bayan mamayar da jami'ansa suka kai majalisar dokokin kasar wadda ya haifar da rudani da tashin hankali.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel