Jam'iyyu 6 na Siyasa sun sha alwashin tallafawa Matasan 'Yan Takara

Jam'iyyu 6 na Siyasa sun sha alwashin tallafawa Matasan 'Yan Takara

Za ku ji cewa a ranar Larabar da ta gabata ne wasu jam'iyyu shida na siyasa, suka alwashin tallafawa matasa dake tsakanin shekaru 18 zuwa 35 masu sha'awar neman takara ta kujerun siyasa daban-daban a babban zabe na 2019.

Kamar yadda shafin jaridar Premium Times ya ruwaito, wadannan jam'iyyu sun hadar da; Accord Party (AP), Action Alliance (AA), Allied Congress Party of Nigeria (ACPN), Better Nigeria Progressive Party (BNPP), Democratic People’s Party (DPP) da kuma National Democratic Congress Party (NDCP).

Jam'iyyun su lashi takobbi cikin gamammiyar sanarwa a babban birnin tarayya na Abuja, yayin da wata kungiya mai zaman kanta ta gudanar da wani taro kan ci gaban kasa tare da wasu matasa masu sha'awar takara a yankin Arewa ta Tsakiya.

Jam'iyyu 6 na Siyasa sun sha alwashin tallafawa Matasan 'Yan Takara

Jam'iyyu 6 na Siyasa sun sha alwashin tallafawa Matasan 'Yan Takara

Legit.ng ta fahimci cewa, jam'iyyun sun yi wannan kira ne domin karfafawa matasa wajen damawa da su cikin harkokin siyasa tare da rike mukamai daban-daban a kasar nan.

A sanadiyar haka ne jam'iyyun suka kudirci yiwa matasa rahusa ta sayen takardun tsayawa takara domin samun kwarin gwiwa kamar yadda shugabannin jam'iyyun AP, ACPN da kuma BNPP na kasa suka bayyana.

KARANTA KUMA: Tinubu ya caccaki Tsohon Shugaban 'Kasa, Obasanjo, kan Wasiƙun sa ga Shugaba Buhari

Shugabannin jam'iyyu uku da suka rattaba hannu kan wannan kudirin sun hadar da; Lawal Nalado na AP, Gani Galadima na ACPN da kuma Nnaji Godswill na jam'iyyar BNPP.

Sun kuma yi kira kan tanadin na yawan adadin mukamai ga matasa tare da basu dama ta taka rawa cikin harkoki da shawarwari na siyasa a fadin kasar nan.

Watanni kadan da suka gabbata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan sabuwar dokar nan da take baiwa matasa dama ta damawa cikin harkokin siyasa domin ci gaban kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel