Da dumi dumi: Mayakan kungiyar Boko Haram sun halaka wani jami’in hukumar NEMA

Da dumi dumi: Mayakan kungiyar Boko Haram sun halaka wani jami’in hukumar NEMA

Kungiyar ta’addanci ta Boko Haram ta halaka wani babban jami’in hukumar bada agajin gaggawa, NEMA, mai suna John Iliya a ranar Laraba, 8 ga watan Agusta, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban sashin watsa labaru na hukumar, Sani Datti ne ya sanar da haka a ranar Alhamis, 9 ga watan Agsuta, inda yace Iliya na tuka motar dake hakar kasa ne don gina ma Sojoji ramukan buya a jihar Borno.

KU KARANTA: Hawainiyarka ta kiyayi ramar Baba Buhari – Iyaye Mata ga Obasanjo

Datti yace a yanzu haka kafatanin ma’aikatan hukumar NEMA sun fada cikin halin alhini da juyayin mutuwar mamacin, wanda suka bayyana shi a matsayin mutumin kirki, wand bashi da matsala da kowa a hukumar.

Sai dai Kaakakin bai yi karin haske game da yadda aka kashe John ba, amma yace tuni shugaban hukumar NEMA, Mustapha Maihaja ya tura da tawagar jami’an hukumar don su dauko iyalan John daga Maiduguri.

A wani labarin kuma, Dakarun Sojin Najeriya sun yi watsa watsa da wasu yan bindiga mayakan kungiyar Boko Haram a ranar 5 ga watan Agusta a kauyen Malari, sa’annan suka kwato kekuna guda goma daga wajensu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel