Daruruwan Matasan APC sun gudanar da zanga zangar kin jinin Saraki a Kaduna

Daruruwan Matasan APC sun gudanar da zanga zangar kin jinin Saraki a Kaduna

Daruruwan matasa daga sassan jihar Kaduna sun taru a babban Ofishin jam’iyyar APC dake cikin garin Kaduna inda suka gudanar da zanga zangar kin jinin shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki, inji rahoton Premium Times.

Matasan na jam’iyyar APC sun shirya wannan zanga zanga ne da safiyar Alhamis, 9 ga watan Agusta, duk kuwa da mamakon ruwan sama daya sauka a garin, inda suka bukaci Sanata Saraki ya yi murabus daga kujerar da yake kai a yanzu.

KU KARANTA: Ibrahim Magu ya taso Lawal Daura a gaba bisa zargin satar wasu kudi

Jagoran wannan zanga zanga mai suna Haruna Maikano ya bayyana muradunsu a cikin wata wasika da ya mika ma sakataren jam’iyyar APC a jihar, Mohammed Shuaibu, inda yace ba zasu zura idanu ba alhalin wasu yan kalilan na kokarin kawo tasgaro ga Dimukraddiya.

Daruruwan Matasan APC sun gudanar da zanga zangar kin jinin Saraki a Kaduna

Zanga zangar

Don haka suka yi kira da lokaci yayi da ya kamata a kawar da Saraki daga kujerar, a maye gurbinsa da wani Sanata kwararre, don a matsayinsu nay an Arewa, Saraki ya basu kunya da kamun ludayinsa a majalisar.

Bugu da kari matasan sun bayyana goyon bayansu ga tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, da ya shiga APC a ranar Laraba, 8 ga watan Agusta, Sanata Godswill Akpabio don yam aye gurbin Saraki a matsayin shugaban majalisar dattawa, a cewarsu shine kadai zai iya gyara kurakuren da Saraki ya tafka a shekara uku.

Daga karshe Maikano yace sun aika ma dukkan Sanatocin Arewa wannan wasikar dake dauke da bukatunsu, haka zalika sun yi shirin ganawa da kafatanin Sanataocin don tabbatar musu da matsayansu.

A nasa jawabin, Sakataren APC reshen jihar Kaduna, Mohammed Shuaibu ya bayyana jin dadinsa da yadda matasan suka yi zanga zangarsu cikin doka da ka’ida, kuma ya basu tabbacin wasikarsu zata kai ga shugaban APC na kasa, har ma ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel