2019: Saraki ya gana da shugabannin jam’iyyu 45

2019: Saraki ya gana da shugabannin jam’iyyu 45

Shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, ya yi wata ganawa da shugabannin wasu jam’iyun siyasa 45 a yau, Alhamis, a ofishinsa.

Sarki ne da kansa ya sanar da hakam a cikin wani sako da ya fitar a shafinsa na Tuwita dake dandalin sada zumunta.

Ina wata ganawa yanzu haka da wasu shugabannin jam’iyyu 45 a ofishina,” kamar yadda Saraki din ya rubuta a cikin sakon nasa.

A jiya ne jagoran jam’iyyar APC na kasa, Sanata Ahmed Bola Tinubu, ya yi zargin cewar wasu mambobin majalisar dattijai na yunkurin tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari.

2019: Saraki ya gana da shugabannin jam’iyyu 45

Bukola Saraki

Tinubu ya gargadi masu yunkurin das u gaggauta ajiye wannan kudiri nasu domin ba zai taba samun karbuwa ba tare da kwatanta yunkurin nasu da cewar “tamkar kadangare ne yake kokarin yin kokawa da jimina.”

DUBA WANNAN: Yakin neman zaben APC: Osinbajo ya ziyarci sarkin Daura a fadar sa, duba hotuna

Wadannan kalamai na fitowa daga bakin Tinubu ne yayin da yake gabatar da jawabi ga dandazon jama’ar da suka halarci bikin karbar tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio, biyon bayan canjin shekar da ya yi daga PDP zuwa APC.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel