Tsige Shugaban kasa: Sanatocin Najeriya sun karyata Bola Tinubu

Tsige Shugaban kasa: Sanatocin Najeriya sun karyata Bola Tinubu

Mun samu labari daga Daily Trust cewa Sanatocin babban Jam’iyyar adawa Najeriya na PDP sun karyata Jigon Jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu game da batun da yayi jiya na cewa ana neman tsige Shugaban kasa Buhari a Majalisa.

Tsige Shugaban kasa: Sanatocin Najeriya sun karyata Bola Tinubu

Sanatoci sun ce ba a maganar tsige Shugaban kasa a Majalisa

Sanata Isa Hamma Misau ya karyata maganar Bola Tinubu na cewa ‘Yan Majalisa na neman sauke Shugaban kasa Muhammadu Buhari daga mulki. Sanatan na tsakiyar Bauchi yace Bola Tinubu ya ji dadin fatar bakin sa ne kawai.

Isa Misau ya kore jawabin na tsohon Gwamnan Legas inda yace karya ce kurum ya sharba saboda dalilin sa na siyasa. Sanatan na PDP yace fitaccen ‘Dan siyasa kamar sa bai kamata ya rika magana ba tare da sun auna kalaman su ba.

KU KARANTA: Mataimakin Shugaban kasa ya kai ziyara Jihar Katsina

Bola Tinubu ya fadi wannan ne lokacin da APC tayi wa Godswill Akpabio wankan tsarki a Jihar sa ta Akwa Ibom. Sanatan dai yacce sam bai dace Tinubu a matsayin sa ya rika furta maganganu marasa tushe irin wannan ba.

Misau wanda shi ne Shugaban kwamitin harkar Sojojin ruwa ya kalubalanci Jigon na APC da ya fito yayi baja-kolin hujjoji ba ya rika zuba karya ba. ‘Dan Majalisar dai yace tsarin Damukaradiyya da hakkin jama’a su ke karewa.

A jiya APC mai mulki ta nada tsohon Shugaban marasa rinjaye a Majalisar Dattawa watau Godswill Akpabio a matsayin Shugaban Jam’iyyar a Jihar Akwa-Ibom. Asiwaju Bola Tinubu ya halarci taron.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel