Yakin neman zabe: Osinbajo da wasu gwamnonin arewa sun isa jihar Katsina

Yakin neman zabe: Osinbajo da wasu gwamnonin arewa sun isa jihar Katsina

Mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya isa garin Daura dake jihar Katsina domin yiwa dan takarar sanata a karkashin jam’iyyar APC yakin neman zabe.

Osinbajo ne zai jagoranci tawagar yakin neman zaben sanatan da za a gudanar biyo bayan mutuwar sanatan dake wakiltar yankin, kamar yadda Laolu Akande, mai taimakawa Osinbajo a bangaren yada labarai ya sanar.

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da takwaransa na jihar Katsina, Aminu Bello Masari, suka tarbi Osinbajo bayan ya sauka a Katsina kafin su dunguma su wuce zuwa garin Daura.

DUBA WANNAN: Ana kulla tuggun tsige Buhari - Tinubu

Bayan isar sa garin Daura, Osinbajo ya wuce kai tsaye ya zuwa fadar sarkin garin, Farouk Umar Farouk, domin yin gaisuwa.

"Manufar jam'iyyar APC da gwamnatin shugaba Buhari ita ce inganta rayuwar talakan Najeriya," Osinbajo ya shaidawa sarkin na Daura.

A nasa jawabin, sarkin Daura ya tabbatarwa da Osinbajo cewar mutanensa na tare da shugaba Buhari da kuma gwamnatinsa dari bisa dari.

Yakin neman zabe: Osinbajo da wasu gwamnonin arewa sun isa jihar Katsina

Osinbajo a fadar sarkin Daura

Yakin neman zabe: Osinbajo da wasu gwamnonin arewa sun isa jihar Katsina

Osinbajo da wasu gwamnonin arewa sun isa jihar Katsina

Yakin neman zabe: Osinbajo da wasu gwamnonin arewa sun isa jihar Katsina

Osinbajo a fadar sarkin Daura

Yakin neman zabe: Osinbajo da wasu gwamnonin arewa sun isa jihar Katsina

Osinbajo da Sarkin Daura

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel