‘Yan Najeriya sun bayyana godiyarsu game da sabon jirgin kasan Abuja (Bidiyo)

‘Yan Najeriya sun bayyana godiyarsu game da sabon jirgin kasan Abuja (Bidiyo)

- Bayan kaddamar da jirgin kasan Abuja fasinjoji sun sun ji dadi amma sun bayyana fargaba

- Fargabar tasu na da alaka da yadda acewarsu aka saba shakulatin bangaro da kayayyakin gwamnati a baya

A ranar 12 ga watan Yulin da ya gabata ne shugaban kasa Muhamamdu Buhari ya kaddamar da sabon jirgin kasa mai amfani da wutar lantarki a babban birnin tarayya Abuja, wanda kuma ya kasance irinsa na farko a Nahiyar Afrika.

Duk da yake kashi na farko aka kaiga budewa na aikin, ragowar dayan kashin sai nan gaba, fasinjojin da suka samu damar fara hawa sabon jirgin sun nuna murnarsu da kan yadda aka gudanar da aikin. Sai dai sun bayyana fargabarsu ko gwamnatin Najeriya zata iya alkinta shi.

KU KARANTA: Ta leko ta koma ga ‘yan bautar kasa, ba gaskiya cikin batun karin alawus dinsu zuwa N49,000

Fasinjojin jirgin sun bayyanawa wakilinmu da ya zanta da su cewa, kaddamar da jirgin da yake daidai da na kowacce kasar da ta cigaba a duniya babban abin a yaba ne, amma kuma tsoron yadda aka saba banzantar da kayayyakin gwamnati shi ke basu tsoro.

A don haka ne suka bukaci da gwamnatin tarayya da ta tabbatar ta bi duk matakan da suka dace wajen hana wannan sabon jirgin durkushewa.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel