Tattalin arzikin kasar Iran na kara tabarbarewa bayan Amurka ta karo musu takunkumi

Tattalin arzikin kasar Iran na kara tabarbarewa bayan Amurka ta karo musu takunkumi

- Shekaru biyu aka dauka gurin yarjejeniya da Iran

- A ranar 6 ga watan Augusta ne shugaba Trump ya janye kasar shi daga cikin yarjejeniyar

- Hakan yaci Karo da alkawarin yakin neman zaben da yayi

Tattalin arzikin kasar Iran na kara tabarbarewa bayan Amurka ta karo musu takunkumi

Tattalin arzikin kasar Iran na kara tabarbarewa bayan Amurka ta karo musu takunkumi

Shekaru biyu aka dauka kafin yarjejeniyar nukiliya da kasar Iran ta tabbata, amma lokaci kadan aka dauka gurin warware ta.

A ranar 6 ga watan Augusta ne Donald Trump yasa hannu akan dawo da tsarin hukuncin da na masana'antar mota ta Iran, cinikayyar zinari da kuma samun daloli, kadan daga ciki kenan. Wadannan alkawurran ne yayi, inda a 2015 yasa hannu wanda hakan ne ya bawa kasar Iran kwanciyar hankali akan shirin nukiliya. Dawo da hukuncin kuwa ba zai yi dadi ba.

Yaci Karo da alkawarin da ya dauka a yakin neman zaben shi, inda yace shi kadai ba zai janye daga yarjejeniyar ba domin kasashe biyar ne suka sa hannu, sun hada da Birtaniya, Faransa, Jamus, Rasha da Chana.

A yunkurin kare yarjejeniyar, kungiyar hadin kan Turai ta umarci masana'antun EU da kada su bada hadin kai ga janye yarjejeniyar kuma ta amince dasu kai kara kotu domin bi musu hakki akan abinda Amurka tayi.

Amma kadan daga cikin su suke tunanin hakan zai yi amfani. Masana'antu suna ta daukar barazanar Mista Trump da gaske, na cewa da yayi yin kasuwanci da Iran ba zai bada damar kasuwanci da Amurka ba.

DUBA WANNAN: Manhajar tantance wa'azi a Saudiyya

Total, kamfanin Faransa ya na gab da janye yarjejeniyar aikin da zasuyi na dala biliyan 2 da Iran na babban South Pars Gasfield.

Airbus zata tsayar da kai jirage masu daukar mutane dari, Masana'antun Amurka kamar su Boeing, sun janye kwangilar su ta dala biliyan 20.

Wannan abu ya kawo faduwar darajar kudin Iran. A shekarar da ta gabata, dala daya dai dai take da Rial 38,000 a kasuwa. A yanzu tayi warwas inda darajar Rial din ya rasa gurin kashi 60 cikin dari nashi. A ranar 30 ga watan yuli, dala daya tana dai dai da Rial 119,000. Hakan ya jawo tashin kayan abinci inda suka ninka fiye da kudin su.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel