Sharhi: Tsakanin siyasar majalisun Amurka da ta majalisun Najeriya

Sharhi: Tsakanin siyasar majalisun Amurka da ta majalisun Najeriya

- Amurka siyasa da dimokuradiyyar Najeriya ke kwaikwaya

- Majalisun Amurka sunfi shugaban kasa karfi, a Najeriya abin ba haka yake ba

- Babu wani sauyin sheka ko tsige shugabancin majalisa don jam'iyya ta banbanta

Sharhi: Tsakanin siyasar majalisun Amurka da ta majalisun Najeriya

Sharhi: Tsakanin siyasar majalisun Amurka da ta majalisun Najeriya

A Amurka, inda muka kwapo siyasar dimokuradiyya, akwai jam'iyyu biyu wadanda suka mamaye siyasar kasar, watau Democrats, masu sassaucin ra'ayi da bin tafarkin santsi, da kuma Republicans, watau masu ra'ayin 'yan mazan jiya, ko tabo.

A wannan dalili ne yasa, ko me ake yi, da wuya mutum yana cikin wannan jam'iyya ya sauya ya koma wata don cimma burin siyasa.

A gefe guda kuma, a majalisar dattijai, babu shugaban majalisa, saboda mataimakin shugaban kasa yana da kujerar din-dindin a majalisar dattijai, kuma shine shugaban ta.

DUBA WANNAN: Manhajar tantance wa'azi a Saudiyya

A siyasar Amurka, maimakon irin tamu ta neman kudi, ra'ayinka ra'ayi ne da bazaka sauya ba, saboda kana sauya wa, jama'arka zasu kiranyo ka, su nemo wani su aika, don kare nasu muradun.

Wannan ta nuna siyasar Najeriya ba wai kawai masu ilimin siyasa da na boko take so ba, a'a, tana kuma son masu zaben ma ya zama suna da ilimi da ma fahimtar me suke so, ba wai a watsa musu kudi ne kawai ba.

A lokuta da dama, takan kasance bangaren gwamnati ya zamo yana hannun jam'iyya daya, amma bangaren majalisu ko ta wakilai ko ta dattijai ta zama tana hannun wata jam'iyyar, wadda kan wahal da shugaban kasa.

Su Sanatoci jihar su da gwamnati suke wakilta, inda ita kuma majalisar wakilai jama'a da gunduma take wakilta.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel