Yanzu Yanzu: Bamu daskarar da kowani asusun bankin Akwa Ibom ba - EFCC

Yanzu Yanzu: Bamu daskarar da kowani asusun bankin Akwa Ibom ba - EFCC

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta bayyana cewa bata daskarar da kowani asusun banki mallakar gwamnatin jihar Akwa Ibom ba.

Hukumar ta wanke kanta kan lamarin bayan ikirari da kwamishinan bayanai na jihar, Charles Udoh yayi a ranar Laraba cewa hukumar yaki da rashawa ta daskarar da asusun jihar.

“Gwamnatin jihar zata yi Magana akan daskarar da asusun nan bada jimawa ba,” cewar Mista Udoh ba tare da ya bada da cikakken bayani ba.

Yanzu Yanzu: Bamu daskarar da ko wani asusun bankin Akwa Ibom ba - EFCC

Yanzu Yanzu: Bamu daskarar da ko wani asusun bankin Akwa Ibom ba - EFCC

Amma wani babban jami’in EFCC ta bayyanawa majiyarmu a ranar Alhamis cewa hukumar bata daskarar da kowani asusu mallakar gwamnatin jihar ba a gida ko a wajen Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Yan majalisan APC 8 sun yi barazanar sauya sheka a Edo

Ya kalubalanci kwamishinan bayanan da ya ba da cikakken bayanin asusun da suke ikirarin an daskararar.

Yace babu bukatar daskarar da asusun tunda gwamnatin jihar da hukumar na shari’a a kotu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel