Sakamakon zaben 2019 zai bar masu sauya sheka cikin danasani – Sheriff

Sakamakon zaben 2019 zai bar masu sauya sheka cikin danasani – Sheriff

Shugaban kwamitin magoya bayan shugaban kasa, Sanata Ali Modu Sheriff ya bayyana cewa sakamakon zaben 2019 zai kunyata dukkanin masu sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki zuwa sauran jam’iyyu.

Yayinda ya karbi bakuncin mambobin kwamitin PSC a Abuja, Sheriff, tsohon shugaban PDP yace kudirinsa shine tabbatar da cewa an sake zabar shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019.

Yace ya yanke shawarar kin hada lamura da wasu mutane a lokacin da cece-kuce ya taso kan kafa kwamitin PSC da kuma zabarsa a matsayin shugaban kungiyar sakamakon son da yake yiwa shugaba Buhari.

Sakamakon zaben 2019 zai bar masu sauya sheka cikin danasani – Sheriff

Sakamakon zaben 2019 zai bar masu sauya sheka cikin danasani – Sheriff

“Kudirina shine son ganin an sake zabar shugaba Buhari a 2019. Wadanda suka bar jam’iyyar sunyi gagarumin kuskure sannan kuma ina da yakinin cewa ficewarsu zai taimaki jam’iyyar,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: Yan majalisan APC 8 sun yi barazanar sauya sheka a Edo

Ya kara da cewa akwai bukatar jam’iyya mai mulki ta shirya gidanta domin ta samu damar cin zaben 2019 cikin kwanciyar hankali.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel