Badakalar N369m: Hukuma ta gayyaci Sanata Hunkuyi

Badakalar N369m: Hukuma ta gayyaci Sanata Hunkuyi

Hukumar yan sandan Najeriya ta sammaci sanata mai wakiltar Kaduna ta Arewa kuma dan takarar gwamnan jihar, Sanata Suleiman Usman Hunkuyi.

Hukumar yan sandan a wata wasika da ta aika ranan 3 ga watan Agusta ta bukaci sanatan ya bayyana gaban jami’in dan sanda, DSP Ibrahim Agu domin bayani kan kudin da suke bincike.

A wasikar mai lamba AR:300/IGP.SEC/MU/STS/FHQ/ABJ.T.A/VOL.9 ta bukace shi ya bayyana a ranan Laraba, 8 ga watan Agusta 2018 a hedkwatan hukumar da ke Abuja.

KU KARANTA: Tsohon hadimin shugaban DSS ya fallasa yadda yake karbar cin hanci da rashawa

Tace: “ Wannan ofishin na binciken wani zargin almundahana, cuta, damfara da rashawa da kokarin karkatar da dukiya.”

Jaridar Punch ta samu rahoton cewa an gayyacesa ne bisa ga wani kara da aka kaiwa sifeto janar na hukumar yan sanda, Ibrahim Idris, kan kudi N369m na fili da ke Indepence way, jihar Kaduna.

Game da cewar karar, an yi wani ciniki ne wanda ya kunshi gina kasuwa a wani sashen filin. Wakilar kungiyar kwadagon Najeriya, shiyar jihar Kaduna sun je filin kuma sun bukaci amsoshi kan wanda ya nada umurnin gini a kan filin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel