Kaico: Iyaye sun hada baki sun sayar da jaririnsu N400,000

Kaico: Iyaye sun hada baki sun sayar da jaririnsu N400,000

- Dubun wasu iyaye da suka sayar da jaririnsu ta cika, jami'an tsaro sunyi ram da su

- Mijin matar ya ce yayi niyyar siyan babur ne da kudin da za'a ba shi

'Yan sanda a jihar Imo sun cafke wasu mata da miji Ugochukwu Nwachukwu da Glory Nwachukwu bisa alifin sayar da jaririnsu dan watanni hudu da haihuwa kan kudi Naira dubu dari hudu (400,000).

Allah wadaran naka ya lalace: Idon wasu Mata da Miji ya rana fata bayan kama su sun sayar da jaririnsu N400,000

Allah wadaran naka ya lalace: Idon wasu Mata da Miji ya rana fata bayan kama su sun sayar da jaririnsu N400,000

Da yake holar iyayen jaririn a shelkwatar ‘yan sanda ta kasa reshen jihar ta Imo dake Owerri a jiya Laraba, kwamishinan ‘yan sanda na jihar Dasuki Galadanchi, ya ce iyalan 'yan yankin Umueme Obike dake a karamar hukumar Ngor Okpala.

KU KARANTA: Shegiyar uwa: Yadda wata mata ta yi karyar sace ta da ‘yarta don damfari mijinta miliyan N15m

Kuma bayan aika-aikar sayar da dan nasu da suka yi, sun sake hada baki suka yaudari wata mata suka sace yara mata 'ya'ya biyu suka sayar da su.

Kwamishinan ya kara da cewa, “Jami’an rundunar masu yaki da ‘yan garkuwa da mutane ne suka damko su a ranar 20 ga watan Yuli a yankin Owerre-Nta dake karamar Isiala Ngwa cikin jihar Abia. Tuni suka amince da aikata laifin yin safarar mutane da sauran laifuka a fadin jihar ta Imo.”

Galadanchi ya kuma shaida cewa yanzu haka rundunar ‘yan sandan na cigaba da farautar ragowar abokan aikata laifukan na kungiyar da suka tsere.

Sai dai Ugochukwu ya shaidawa manema labarai cewa ya sayar dan nasa kan kudi Naira N400,000 ne saboda tsananin matsin rayuwa da suke fama da shi don ta siyi babur.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel