Fashin Offa: IGP ya samu umurnin kotu kan aika sammaci ga Saraki

Fashin Offa: IGP ya samu umurnin kotu kan aika sammaci ga Saraki

Sufeto janar na yan sanda, Ibrahim Idris ya samu damar aika sammaci ga shugaban majalisar dattawa akan fashin Offa.

A wata wasika daga Barista Oliwatosin Ojaomo ya aika ga sufeto janar na yan sanda ya nemi a aika sammacin gaggawa ga shugaban majalisar dattawa kamar yadda sashi na 122 na dokar laifi na 2015 ya tanadar.

An bayar da damar ne a ranar 31 ga watan Yuli daga kotun Grade One Area Court, ACO Estate, Lugbe, Abuja dauke da lambar shari’a : CR/196/18 tsakanin Ojaomo da Bukola Saraki.

Fashin Offa: IGP ya samu umurnin kotu kan aika sammaci ga Saraki

Fashin Offa: IGP ya samu umurnin kotu kan aika sammaci ga Saraki

Lauyan ya zargi Saraki, wadda yaki amsa gayyatar IGP a ranar 24 ga watan Yuli, 2018, “da kawo cikas wajen gudanar da biciken laifi sannan ya ki mutunta jami’in gwaamnati wadda ke gudanar da aikin doka” hakan kuma laifi ne a sashi na 136 da 149.

KU KARANTA KUMA: APC, sun cinnawa tsinsiya wuta a Nasarawa

An sanya shari’ar a ranar 10 ga watan Satumba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel