Zaben 2019: Ba bu wani 'Dan Takara na PDP da zai iya nasara akan Buhari - Fadar Shugaban 'Kasa

Zaben 2019: Ba bu wani 'Dan Takara na PDP da zai iya nasara akan Buhari - Fadar Shugaban 'Kasa

Mun samu rahoton cewa, mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, yana cikakken tabbacin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi nasara kan duk wani dan takarar kujerar sa domin ci gaba da dabbaka akidar sa ta canji da kawo sauyi a kasar nan.

A ranar da ta gabata ne mukaddashin shugaban kasar ya bayyana hakan cikin birnin Ikot Ekpene dake jihar Akwa Ibom, a yayin yiwa Sanata Godswill Akpabio lale maraba da ya sauya sheka daga jam'iyyar adawa ta PDP zuwa APC.

Mukaddashin shugaban kasar wanda sakataren gwamnatin tarayya ya wakilta, Boss Mustapha ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin shugaba Buhari ba za ta ci gaba da tafiyar ta da masu yasar dukiya cikin asusun gwamnati.

Zaben 2019: Ba bu wani 'Dan Takara na PDP da zai iya nasara akan Buhari - Fadar Shugaban 'Kasa

Zaben 2019: Ba bu wani 'Dan Takara na PDP da zai iya nasara akan Buhari - Fadar Shugaban 'Kasa

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya bayyana, jihar ta Akwa Ibom ta tumbatsa yayin karbar Sanata Akpabio inda jiga-jigan jam'iyyar da dama suka halarta da suka hadar da; shugaban jam'iyyar na kasa Adams Oshiomhole, kanwa uwar gamin matsalolin jam'iyyar, Asiwaju Bola Tinubu.

Sauran wadanda suka halarta sun hadar da; gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki, Sanata Ita Enang, Sanata Ahmed Lawan da ya jagoranci tawagar sanatoci 35, shugaban hukumar NDDC, Nsima Ekere da sauran jiga-jigai na jam'iyyar.

KARANTA KUMA: Kotu ta gindayawa Saraki Katanga tsakanin sa da Lauyan kolu da Sufeto Janar na 'Yan sanda

Rahotanni sun bayyana cewa, Oshiomhole ya kuma bayar da sanarwa ta kaddamar da tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Sanata Akapabio a matsayin sabon shugaban jam'iyyar na jihar.

A nasa bangaren Mataimakin shugaban kasar ya jinjinawa al'ummar Akwa Ibom da suka yi cincirindon nuna goyon baya tare da yabawa Sanata Akpabio dangane da wannan shawara da ya yanke ta sauya sheka sakamakon tasirin hakan ga yankin kudancin kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel