Kwastam tayi babbar nasarar damke maganin Kodin, tsala-tsalan motoci da wasu mutane 8

Kwastam tayi babbar nasarar damke maganin Kodin, tsala-tsalan motoci da wasu mutane 8

- Sau biyu kenan Kwastam na samun nasarar kama maganin tari na ruwa Kodin tun bayan haramta shigowa da sarrarafawa tare da ta’ammali da shi

- Kayayyakin biliyoyin kudi da mutane takwas da ake zargi sun shiga hannun jami’an na Kwastam

Jami'an hukumar hana fasa kwauri ta kasa sun kama wadansu kayayyaki wadanda adadin kudinsu ya kai sama da Naira biliyan 1 a cikin kasa da wata daya.

Kwastam tayi babbar nasarar damke maganin Kodin, tsala-tsalan motoci da wasu mutane 8

Kwastam tayi babbar nasarar damke maganin Kodin, tsala-tsalan motoci da wasu mutane 8

Babban jami'in hukumar mai kula da shiyya ta daya Mohammed Uba ne ya sanarwa da manema labarai hakan a jiya Talata, a Ikeja da ke jihar Lagos.

Ya kara da cewa bayan nasarar damke wadannan kayayyakin hukumar ta sake kama wadansu motoci na alfarma guda 17.

KU KARANTA: Tun kafin ai nisa EFCC ta fara bincikar Fayose da matarsa

Cikin Motococin da aka kama an samu wata mai lambar jihar Edo makare da maganin tari na ruwa mai dauke da sinadarin kodin, wanda gwamnatin tarayyar kasar nan ta haramta shigo da shi.

Motar tana dauke da katan din maganin tarin guda 2,784 mai karfin milgiram 100 tare da ware kwaya da aka haramta amfani da ita adadin katan 92.

Jami'an hukumar fasa kwaurin sun samu nasarar damke wannan motar ne a shatale-talen Egbeda dake yankin Afromedia wanda ke kusa da kasuwar Alaban ta jihar Lagos.

Wannan shi ne karo na biyu da hukumar ta samu nasarar damke maganin tarin da ake kokarin shigowa da shi, tun bayan da gwamnatin kasar nan ta haramta shigowa da shi.

Mutane takwas ne ya zuwa yanzu aka damke wadanda ake zargin suna da hannu a cikin wannan badakala.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel