Yan majalisan APC 8 sun yi barazanar sauya sheka a Edo

Yan majalisan APC 8 sun yi barazanar sauya sheka a Edo

Guguwar sauye-sauyen sheka dake kadawa a fadin kasar ta garzaya mahaifar shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole yayinda yan majalisar dokokin jihar Edo guda takwas suka yi barazanar barin APC zuwa wasu jam’iyyun siyasa.

Babu tabbacin jam’iyyun siyasar da yan majalisar ke shirin komawa a lokaci wannan rahoton, sai dai majiyoyi sun bayyana cewa yan majalisar na shirin sauya sheka ne saboda basu da tabbacin samun tikitin APC.

Wata majiya ta kusa day an majalisar dake shirin barin APC, ya kasance saboda shirin hana yakin neman zabe da shugaban APC na Edo ke yi, acewarsa, hakan ya haifar da tsoro ga yan majalisar cewa lokaci na iya kure masu da za’a zabe su a sauran jam’iyyu idan har basu samu tikitin APC ba.

Yan majalisan APC 8 sun yi barazanar sauya sheka a Edo

Yan majalisan APC 8 sun yi barazanar sauya sheka a Edo

Daya daga cikin yan majalisar jihar dake shirin sauya sheka wadda ya nemi a boye sunansa, ya daura laifin yawan sauya sheka da ake samu a jam’iyyar kan rashin iya siyana da Gwamna Godwin Obaseki.

KU KARANTA KUMA: Magoya bayan Kwankwasiyya sun bar APC, sun cinnawa tsinsiya wuta a Nasarawa

Yace mafi akasarin ayyukan mazabu ba Obaseki ne ke daukar nauyinsu ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel