Akpabio: Zakka ce muka fitar wa jam'iyyar APC - inji jigo a jam'iyyar PDP

Akpabio: Zakka ce muka fitar wa jam'iyyar APC - inji jigo a jam'iyyar PDP

Shugaban kwamitin amintattu na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP Sanata Walid jibril ya ce jam'iyyar ta su cikin karamcin ta ne yasa suka fitar da zakkar Sanata Godswill Akpabio suka baiwa jam'iyyar All Progressive Congress, APC.

Sanata Jibril ya kuma kara da cewa jama'a za su fahimci hakan sosai musamman ma idan suka yi la'akari da cewa shi Akpabio din da shugaban marasa rinjaye ne a majalisar wanda yanzu kuma PDP itace ke da rinjaye, don haka basu bukatar sa.

Akpabio: Zakka ce muka fitar wa jam'iyyar APC - inji jigo a jam'iyyar PDP

Akpabio: Zakka ce muka fitar wa jam'iyyar APC - inji jigo a jam'iyyar PDP

KU KARANTA: Wani Sanatan PDP yayi karin haske game da komawar sa APC

Legit.ng ta samu cewa ya kuma cewa halin dattakun da mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya nuna wajen cire Lawal Daura ma dai kadai ya isa jam'iyyar ta yaba masu wannan ne ma ya sa suka ce bari su basu Akpabio din.

A wani labarin kuma, Shugaban babbar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, PDP Mista Uche Secondus a Najeriya ya ce su fa sun san dukkan dalilan da suka sa tsohon Gwamnan jihar Akwa Ibom, Sanata Godswill Akpabio barin jam'iyyar tasu zuwa APC.

Cif Secondus din dai ko da yake bai bayar da cikakken dalilin sa na fadar hakan ba amma dai ya ce ko kusa komawar ta sa ba ta da alaka da talaka kawai dai don kashin kansa ne yayi hakan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel