Ba dan-ba dan ba da na tsere daga Jam’iyyar PDP – Tsohon Gwamna Uduaghan

Ba dan-ba dan ba da na tsere daga Jam’iyyar PDP – Tsohon Gwamna Uduaghan

- Tsohon Gwamnan PDP ya bayyana abin da ya hana sa komawa Jam’iyyar APC

- Emmanuel Uduaghan yace saboda irin su Ibori da Okowa yayi zaman sa a PDP

- Tsohon Gwamnan yace ba don haka ba da yayi takarar Sanata a APC a 2019

Ba dan-ba dan ba da na tsere daga Jam’iyyar PDP – Tsohon Gwamna Uduaghan

Tsohon Gwamna Emmanuel Uduaghan yayi tunanin barin PDP

Mun samu labari cewa tsohon Gwamnan Jihar Delta Emmanuel Uduaghan da yayi mulki a karkashin Jam’iyyar PDP mai adawa a Kasar nan ya bayyana abin da ya hana sa canza sheka ya koma Jam’iyyar APC duk da cewa wasu na barin PDP a halin yanzu.

Tsohon Gwamna a lokacin PDP ya bayyana babban abin da ya hana sa komawa Jam’iyyar APC yayi takarar kujerar Sanata. Emmanuel Uduaghan yace irin su tsohon Gwamna James Ibori da kuma Gwamna Ifeanyi Okowa su ka sa bai koma APC ba.

KU KARANTA: Abin da ya sa Akpabio ya koma APC - Inji PDP

Emmanuel Uduaghan yace in ba don James Ibori wanda ya mulki Jihar tsakanin 1999-2007 da kuma Gwamna mai-ci Ifeanyi Okowa sun sa baki ba da yanzu yana APC. Tsohon Gwamnan yace yanzu ya fasa sauya-shekar kuma zai yi zaman sa a PDP.

Emmanuel Uduaghan wanda ya bar kujerar Gwamna a 2015 ya nemi ya bar PDP ya koma Jam’iyyar APC domin yayi takarar kujerar Sanatan Delta ta Kudu. Manyan PDP ne su ka sa baki ya canza shawara kamar yadda labari ya zo mana dazu nan.

Dazu kun ji cewa an yi wa tsohon Gwamnan Akwa watau Godwill Akpabio wankan shigowa Jam’iyyar APC. Shugaban Jam’iyyar APC ya nemi tsohon Gwamnan yayi amfani da dukiyar sa da kuma kwarewar sa a Akwa Ibom da ke Kudancin Kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel