Shugaban APC ya caccaki Saraki da PDP bayan Akpabio ya koma APC

Shugaban APC ya caccaki Saraki da PDP bayan Akpabio ya koma APC

Mun samu labari cewa Jam’iyyar APC mai mulki ta nada tsohon Shugaban marasa rinjaye a Majalisar Dattawan Najeriya watau Sanata Godswill Akpabio a matsayin Shugaban Jam’iyyar a Jihar Akwa-Ibom.

Shugaban APC ya caccaki Saraki da PDP bayan Akpabio ya koma APC

Cincirondon Jama'a a wajen bikin sauyin shekar Sanata Akpabio

Jam’iyyar APC ta ba tsohon Gwamnan Jihar Akwa-Ibom watau Godwill Akpabio wannan mukami ne da barin sa PDP a makon nan. A jiya ne dai ta tabbata cewa babban Sanatan ya tsere daga Jam’iyyar PDP ya koma APC mai mulki.

Adams Oshimhole ya bayyana cewa Godswill Akpabio ne Jagoran APC a Jihar sa ta Akwa Ibom, inda ya kuma nemi tsohon Gwamnan Jihar yayi amfani da dukiyar sa da kwarewar sa a siyasa wajen taimakon APC a Kudacin kasar.

KU KARANTA: APC na kokarin nada Akpabio a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa

Shugaban Jam’iyyar ta APC Adams Oshimhole ya kuma caccaki Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki inda yace ya gaza rike Majalisar kasar. Oshimhole ya kuma yi kaca-kaca da Jam’iyyar PDP wanda yace lemar ta kece.

An yi wa tsohon Gwamnan wankan shigowa Jam’iyyar APC ne a filin wasa na Ikot-Ekpene da ke cikin Jihar. Manyan Jam’iyyar sun yi murnar shigowar Akpabio APC wanda su ka ce sauyin-shekar sa duk ya wanke wanda aka yi a baya.

A wajen taron Shugaban Adams Oshimhole yace Jam’iyyar PDP ce ta kashe kasar nan a tsawon shekaru 16 da tayi tana mulki. Wadanda su ke wajen sun hada da; Asiwaju Bola Tinubu; Lai Mohammed; Ahmed Lawan da wasu Sanatocin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel