Mun san komai: Shugaban jam'iyyar PDP ya fallasa dalilin komawar Akpabio APC

Mun san komai: Shugaban jam'iyyar PDP ya fallasa dalilin komawar Akpabio APC

Shugaban babbar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, PDP Mista Uche Secondus a Najeriya ya ce su fa sun san dukkan dalilan da suka sa tsohon Gwamnan jihar Akwa Ibom, Sanata Godswill Akpabio barin jam'iyyar tasu zuwa APC.

Cif Secondus din dai ko da yake bai bayar da cikakken dalilin sa na fadar hakan ba amma dai ya ce ko kusa komawar ta sa ba ta da alaka da talaka kawai dai don kashin kansa ne yayi hakan.

Mun san komai: Shugaban jam'iyyar PDP ya fallasa dalilin komawar Akpabio APC

Mun san komai: Shugaban jam'iyyar PDP ya fallasa dalilin komawar Akpabio APC
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Yadda ta kaya tsakanin Buhari da Osinbajo kafin korar Lawal Daura

Legit.ng ta samu cewa a cikin sanarwar da mataimakin sa akan harkokin watsa labarai ya fitar, ya bayyana fitar ta sa daga jam'iyyar APC a matsayin tamkar caca da ba zata kai shi ko ina ba.

A wani labarin kuma, Tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisar dattijai kuma Sanata daga jihar Akwa-Ibom dake a shiyyar kudu maso kudancin Najeriya Godswill Akpabio a karon farko ya fito karara ya fadi dalilin da yasa ya canza sheka daga PDP zuwa APC.

Godswill Akpabio dai ya bayyana cewa irin tsabar gaskiya da rikon amanar shugaba Buhari tare kuma da halin sa na nuna rashin bangaranci a mulkin sa ne kadan daga cikin dalilan da yasa ya yanke shawarar sauya sheka zuwa APC din.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel