Ba kanta: An kama sojan kasar Amurka ya tafka ta'asa a Najeriya

Ba kanta: An kama sojan kasar Amurka ya tafka ta'asa a Najeriya

Jami'an rundunar nan ta musamman ta yan sandan Najeriya dake yaki da fashi da makami watau Federal Special Anti Robbery Squad dake a jihar Imo ta sanar da samun nasarar cafke wani soja ba'amurke da laifin zamba cikin aminci.

Kwamishinan 'yan sandan jihar ne dai Mista Mr. Dasuki Galadanchi ya sanar da hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba a garin Owerri dake zaman babban birnin jihar.

Ba kanta: An kama sojan kasar Amurka ya tafka ta'asa a Najeriya

Ba kanta: An kama sojan kasar Amurka ya tafka ta'asa a Najeriya

KU KARANTA: Firar Osinbajo da Buhari kafin korar Lawal daura

Legit.ng ta samu cewa kwamishinan ya kara da cewa sojan mai suna Mista Garrick Michael sun kama shi ne da laifin karbar wa wasu 'yan Najeriya kudi da sunan zai samar masu bizar fita.

A wani labarin kuma, Rundunar dakarun sojin Najeriya dake sintirin tabbatar da tsaro da samar da zaman lafiya a jahohin Arewa ta tsakiya a ranar Asabar din da ta gabata sun sanar da yin kicibis da wasu 'yan bindiga a karamar hukumar Guma ta jihar Benue.

Sanarwar afkuwar hakan dai ta fito ne dauke da sa hannun jami'in hulda da jama'a na hedikwatar rundunar dake Abuja, Texas Chuku inda yace kuma dakarun nasu sun yi dauki ba dadi da 'yan bindigar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel