An nemi Gwamnati ta fito da Shugaban Kungiyar IPOB Nnamdi Kanu

An nemi Gwamnati ta fito da Shugaban Kungiyar IPOB Nnamdi Kanu

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ‘Yan Kungiyar nan da ke fafutukar Biyafara watau IPOB sun zauna da Manyan Kasar Inyamurai kwanan nan inda su ka nemi a fito masu da shugaban su Nnamdi Kanu.

An nemi Gwamnati ta fito da Shugaban Kungiyar IPOB Nnamdi Kanu

An rasa inda Nnamdi Kanu ya shige tun bara

Kungiyar IPOB ta gindayawa Gwamnatin Kasar sabon sharadi na cewa ta fito da Nnamdi Kanu wanda har yanzu babu wanda ya san inda yake. Rabon da a ji labarin Kanu tun lokacin da Sojoji su ka shiga gidan sa da ke Jihar Abia.

Manyan Kasar Inyamurai sun gana da ‘Yan Kungiyar ta Biyafara a Garin Enugu inda ake cigaba da tattaunawa domin ganin an samu jituwa da zaman lafiya tsakanin Kungiyar ta IPOB da Gwamnatin Tarayya da sauran jama’a.

KU KARANTA: Shekarau ya gana da wani rikakken 'Dan adawar Buhari

Daga cikin wadanda su ka halarci wannan zama da aka yi kwanan nan wanda Ben Nwabueze ya shirya akwai Nnia Nwodo, Sarkin Onitsa, Igwe Alfred Achebe, Ben Obi, Uzodinma Nwala, Elo Amucheaz, Peter Obi da kuma Lauyan IPOB.

Lauyan Kungiyar Aloy Ejimakor ya bayyanawa ‘Yan Jarida bayan taron da aka yi a wani katafaren otel cewa dole a fito da Nnamdi Kanu domin kuwa ba za ace yayi dabo ba. Kungiyar na zargin Gwamnati da boye Jagoran na ta tun bara.

A shekarar bara 2017 ne Sojojin Najeriya su ka sa Kungiyar IPOB cikin jerin Kungiyoyin ta’addanci a Kasar, hakan dai ya jawo an rasa mutane da dama a Yankin a arangamar da Sojoji su kayi da ‘Yan kungiyar da ke neman kasar Biyafara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel