Hawainiyarka ta kiyayi ramar Baba Buhari – Iyaye Mata ga Obasanjo

Hawainiyarka ta kiyayi ramar Baba Buhari – Iyaye Mata ga Obasanjo

Daruruwan Mata a ranar Laraba, 8 ga watan Agusta sun gudanar da wata zanga zangar nuna goyon baya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a jihar Legas, inda suka ja kunnen tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya fita daga idanun Buhari.

Daily Trust ta ruwaito shugaban kungiyar Africa women Arsie for Change, Josephine Okpara ce ta jagoranci wannan zanga zangar, inda mata dauke da takardu masu kunshe da jawabai daban daban suka diran ma tashar yanci dake Ojota na jihar Legas.

KU KARANTA: Ga lada ga la’ada: Wani Dan kasar China ya auri Bahaushiya bayan ya Musulunta a Filato

Okpara tace: “Mun shirya wannan zanga zanga ne domin tuna ma jama’a kada su yarda shuwagabannin da suka yi kokarin lalata Najeriya a baya su samu nasara, shuwagabannin na son yi amfani da yaki da rashawa wajen tunzura jama’a.”

Hawainiyarka ta kiyayi ramar Baba Buhari – Iyaye Mata ga Obasanjo

Kungiyar Mata

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Okpara na cewa shugaba Buhari ya nuna jarumta ta yadda ya sauya al’amari a tsarin shugabancin Najeriya, haka zalika tace yaki da rashawa da Buhari ya kaddamar ya kwato makudan kudade daga hannun barayi.

Bugu da kari Okpara ya gargadi tsohon shugaba Obasanjo da ya fita daga harkar Buhari, tunda dai shi ya gagara yaki da barayin gwamnati a lokacinsa, tace Obasanjo na amfani da damar mukamin da ya taba rikewa a baya ne wajen cin duddugin gwamnatin Buhari, sakamakon kishin abinda Buhari ke yi, wanda shi bai yi ba a lokacinsa.

“Da ace Obasanjo ya yi shimfida mai kyau a zamaninsa, da Najeriya ta wuce matsayin da take ciki, salon mulkin da Obasanjo ya nuna a zamaninsa yayi ma Najeriya mummunan illa, hakan ya sanya Buhari yake fara komai sabo.” Injita

Hakazalika Okpara ta yi kira ga shugaban kasa da kada ya shakkar Obasanjo, ya kamata ya kaddamar da bincike akansa, sa’annan kada ya karaya da barazanarsa, ya cigaba da yaki da rashawa tare da kama barayin gwamnati.

Daga karshe Okpara ta jaddada goyon bayan kungiyarsu ga shugaba Buhari, tare da aminta da ireiren ayyukan cigaba da yake gudanarwa, sa’annan ta yi kira gareshi da ya cigaba da samar ma yan Najeriya romon Dimukradiyya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel