Kafa da kafa: Shekarau ya yi takakkiya zuwa gidan Fani Kayode, maci mutuncin Arewa

Kafa da kafa: Shekarau ya yi takakkiya zuwa gidan Fani Kayode, maci mutuncin Arewa

Tsohon gwamnan jihar Kano Malam, Ibrahim Shekarau ya bi sawun takwaransa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso wajen kai ma tsohon minista, Femi Fani Kayode ziyara a gidansa dake babban birnin tarayya Abuja.

Legit.ng ta ruwaito Fani Kayode da kansa ya daura hotunan ziyarar da Shekarau ya kai masa, inda ya bayyana cewa yaji dadin karbar bakuntan dan uwansa, sa’annan yace sun tattauna batutun da suka shafi cigaban Najeriya.

KU KARANTA: Babu abin da ka tabuka game da cigabanmu – Matasan jihar Sakkwato ga Tambuwal

Kafa da kafa: Shekarau ya yi takakkiya zuwa gidan Fani Kayode, maci mutuncin Arewa

Ziyarar

“Tsohon ministan ilimi, kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, dan uwana kuma abokina, Malam Ibrahim Shekarau ya karramani da ziyarar da ya kawo gidana dake Abuja, mun tattauna batutuwan cigaba.” Inji shi.

Shi dai Fani Kayode ya shahara wajen cin mutuncin yankin Arewacin Najeriya, al’ummar Hausa Fulani da ma addinin Musulunci gaba daya, kuma bai taba da nasanin abinda yake yi ba, toh amma da yake kakar zabe ake, hakan ka iya bada haske game da ziyarar ta Shekarau.

Kafa da kafa: Shekarau ya yi takakkiya zuwa gidan Fani Kayode, maci mutuncin Arewa

Ziyarar

Ko a kwanakin baya an hangi keyar Sanata Rabiu Kwankwaso a gidan Fani Kayode, haka zalika shima tsohon gwamnan jihar Kaduna, kuma tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Ahmad Makarfi ya kai ma Kayode irin wannan ziyara.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel