Kudi $150m gwamnati zata kashe don sake tisa korar cutar shan inna a bana

Kudi $150m gwamnati zata kashe don sake tisa korar cutar shan inna a bana

- FEC ta amince da aron kayan aiki na dala miliyan 150 don yakar cutar shan inna

- Adeosun tace kasar ta samu kusan kashi 80 cikin dari na rigakafin cutar a kowacce jiha

- Wannan kayayyakin da za'a samu, za'ayi amfani dashi ne gurin tallafawa jihohi 12 da aka bari a baya

Kudi $150m gwamnati zata kashe don sake tisa korar cutar shan inna a bana

Kudi $150m gwamnati zata kashe don sake tisa korar cutar shan inna a bana

Taron zababbun tarayya wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta a ranar laraba a Abuja ya amince da aron kayayyakin dala miliyan 150 a matsayin kokarin gwamnatin tarayya na fatattakar cutar shan inna.

Ministan kudi, Mrs Kemi Adeosun, tayi wa manema labarai bayani bayan taron, tace za'ayi amfani da bashin ne gurin cigaba daga inda aka tsaya na korar cutar ta shan inna.

Adeosun tace kwalliya ta biya kudin sabulu, gani da cewa ana gab da fatattakar cutar ta shan inna. Kayan aikin zasu taimaki gwamnatin tarayya a matsayin yunkurin korar cutar shan inna ta duniya.

Kamar yanda tace, kasar ta samu daidaituwar kashi 80 cikin dari na rigakafin cutar a fadin jihohin kasar.

Adeosun tace za a tabbatar da an tallafawa jihohi 12 da aka barsu a baya wanda suka hada da jihohin Adamawa, Bayelsa, Gombe, Jigawa, Katsina, Kogi, Nasarawa, Niger, Filato, Taraba da Zamfara. Ta kara da cewa cibiyar kiwon lafiya da cigaba (NPHCDA) su zasu shirya yanda aikin zai kasance.

DUBA WANNAN: Komawar Akpabio APC ta dawo mana da duk asarar mu ga PDP

Mista Babatunde Fashola, Ministan wuta, aiyuka da gidaje yace FEC ta yarje da kwangilar titin Akwanga-Jos-Bauchi-Gombe mai Tsawon kilomita 420.6, wanda zai ci Naira biliyan 348.594.

Kamar yanda yace za a bude tagwayen titin babbar hanyar ne. Fashola yace aikin zai dau tsawon wata 48.

Idan zamu tuna FEC ta amince da kwangilar titin Abuja zuwa Keffi tare da titin Akwanga-Lafia-Makurdi na tsakiyar arewa.

Ministan yace titin Enugu-Makurdi ma FEC ta amince da aikin shi, wanda shine zai sada kudu maso gabas zuwa arewa ta tsakiya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel