Gwamnatin Tarayya ta na yiwa Zaɓen 2019 riƙo tamkar wani lamari na Gaggawa - Dogara

Gwamnatin Tarayya ta na yiwa Zaɓen 2019 riƙo tamkar wani lamari na Gaggawa - Dogara

Shugaban majalisar wakilai, Honarabul Yakubu Dogara, ya kalubalanci fadar shugaban kasa da yiwa zaɓen 2019 riƙo tamkar wani lamari mai tsanani na gaggawa.

Dogara ya bayyana hakan ne yayin ganawar majalisar dokoki ta tarayya da kuma Farfesa Mahmoud Yakubu, shugaban hukumar zabe ta kasa watau INEC.

Gwamnatin Tarayya ta na yiwa Zaɓen 2019 riƙo tamkar wani lamari na Gaggawa - Dogara

Gwamnatin Tarayya ta na yiwa Zaɓen 2019 riƙo tamkar wani lamari na Gaggawa - Dogara

A cewar sa, muhimmancin gudanar da wannan ganawa tare da Farfesa Yakubu ya bayu ne sakamakon alhakin ƙaddamar da al'amurran da suka shafi tanadar duk wata bukata ta hukumar zaɓe da ya rataya a wuyan majalisar.

KARANTA KUMA: Wani Matashi ya kashe kansa bayan Budurwar sa ta ƙi amintuwa da buƙatar sa

A yayin bayyana ra'ayin sa, Dogara ya ce ba bu dace dangane da yadda ake yiwa shirin zaɓen 2019 riƙo tamkar wani lamari mai tsanani na gaggawa.

A nasa bangaren, shugaban hukumar zaɓe ya yabawa majalisar tare da godiya dangane da goyon bayan ta wajen aiwatar da shirye-shirye gudanar da zaɓen 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel