Ana kulla tuggun tsige shugaba Buhari – Tinubu

Ana kulla tuggun tsige shugaba Buhari – Tinubu

Jagoran jam’iyyar APC na kasa, Sanata Ahmed Bola Tinubu, ya yi zargin cewar wasu mambobin majalisar dattijai na yunkurin tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Tinubu ya gargadi masu yunkurin das u gaggauta ajiye wannan kudiri nasu domin ba zai taba samun karbuwa ba tare da kwatanta yunkurin nasu da cewar “tamkar kadangare ne yake kokarin yin kokawa da jimina.”

Wadannan kalamai na fitowa daga bakin Tinubu ne yayin da yake gabatar da jawabi ga dandazon jama’ar da suka halarci bikin karbar tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio, biyon bayan canjin shekar da ya yi daga PDP zuwa APC.

Ana kulla tuggun tsige shugaba Buhari – Tinubu

Buhari da Tinubu

Mu muna gwamnati ne don jama’a ba don kudi ko son mulki ba. Wannan shine banbancin mu da jam’iyyar PDP da suka yarda ceware ana neman mulki ne domin tara abin duniya da kuma nuna isa,” a kalamana Tinubu.

Sannan ya cigaba da cewa, “shekara 16 ‘yan Najeriya suka bawa jam’iyyar PDP amma sun kasa kawo canji a rayuwar mutane, sun mayar da hankali ne kawai wajen wawura, handama da babakere a kan dukiyar kasa.”

DUBA WANNAN: Matasa sun yiwa tsohuwa mai shekaru 70 fyade sannan jefe ta har lahira

Kazalika, Tinubu, ya nuna farincikinsa da dawowar Akpabio cikin jam’iyyar APC tare da mika godiya ta musamman ga matarsa, Ekaete Akpabio, bisa goyon bayan da take bawa mijin nata.

A nasa jawabin, Boss Gida Mustapha, sakataren gwamnatin tarayya kuma mutumin da ya wakilci mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya sanar da jama’ar jihar Akwa Ibom cewar shugaba Buhari na kaunar su kamar yadda yake kaunar dukkan ‘yan Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel