Wasu matasa sun bi wata tsohuwa mai shekaru 70 har gida sun jefe ta

Wasu matasa sun bi wata tsohuwa mai shekaru 70 har gida sun jefe ta

Wata tsohuwa, Helen Udugbezi, mai shekaru 70 ta gamu da ajalinta bayan da wasu batagarin matasa suka bi ta har gida suka jefe ta a garin Benin na jihar Edo.

Rahotanni sun bayyana cewar matasan sun yi amfani da wani babban dutse wajen yin jifan day a zama sanadin mutuwar ta.

Anna Amos, wata mai yiwa marigayiya Udugbezi aiki, wacce kuma abin ya faru a kan idonta ta bayyana cewar matasan sun yiwa tsohuwar fyade kafin daga bisani su soke tad a wuka tare da yin amfani da wani babban dutse su jefe ta.

Wasu matasa sun bi wata tsohuwa mai shekaru 70 har gida sun jefe ta

Wasu matasa sun bi wata tsohuwa mai shekaru 70 har gida sun jefe ta

Anna ta kara da cewa said a matasan suka rufe mata idanu tare da daure mata baki kafin su yi mata dukkan ta’addancin da suka aikata.

DUBA WANNAN: Kungiyar matan kabilar Yoruba sun gudanar da tattakin goyon bayan Buhari, sun caccaki Obasanjo

Dag a marigayiyar, Harrison, ya bayyana mamakinsa bisa yadda matasan suka kasha mahaifiyar tasa ta wannan mummunar hanya.

Tuni jami’an ‘yan sanda na ofishin Sabuwar Etete suka dauki gawar Udugbezi zuwa dakin adana gawa tare da fara gudanar da bincike.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel