Shigar Akpabio APC ta dawo mana da duk asarar da muka yi a PDP

Shigar Akpabio APC ta dawo mana da duk asarar da muka yi a PDP

- Canza shekar Godswill Akpabio ta tsayar da canza sheka zuwa PDP

- Godswill Akpabio ya zama daya tamkar 14 kenan

- Koda yake a shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa ya kasance yana kalubantar jam'iyyar PDP

Shigar Akpabio APC ta dawo mana da duk asarar da muka yi a PDP

Shigar Akpabio APC ta dawo mana da duk asarar da muka yi a PDP

Ahmad Lawan, shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa yace canza sheka da Godswill Akpabio yayi daga PDP zuwa APC ya tsayar da komawa da ake jam'iyyar PDP.

Yace tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom din Sanata na daban ne wanda yake da magoya baya a duk fadin kasar nan.

Lawan yayi wannan maganar ne a rally din APC na jihar Akwa Ibom a ranar laraba domin karbar Akpabio zuwa jam'iyya mai mulki.

Kwanan nan jam'iyyar ta rasa sanatoci 14 wanda ya hada da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, ga jam'iyyar PDP.

Amma Lawan yace canza shekar Akpabio duk tafi ta sauran sanatocin.

"Canza shekar Sanata Akpabio ta lashe ta sauran. Daya ce tamkar 14." inji shi.

Wannan sanatan ba daya yake da sauran ba, ya kuma yarda da hadin kan Najeriya, daidaituwar ta da kuma mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari. Ya yarda da cewa yan Najeriya su goyi bayan wannan tafiya.

DUBA WANNAN: N5m ga wanda ya fidda Borno kunya

"Daga wannan lokacin, wannan ya zama Dan jam'iyyar mu ta ko'ina, domin dama namu ne kuma mai kishin kasar mu ne.

Bana kiranshi da shugaban yan adawa, nafi Kiran shi da shugaban marasa rinjaye na majalisar saboda baya adawa da gwamnati. Yana fara duba ra'ayin kasa ne kuma yana adawa mai ma'ana. Koyaushe yana gane cewa daidaituwa da hadin kai muke so."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel