Kungiyar mata ta gudanar da tattakin nuna goyon baya ga Buhari, sun caccaki Obasanjo

Kungiyar mata ta gudanar da tattakin nuna goyon baya ga Buhari, sun caccaki Obasanjo

Wata kungiyar mata (African Women for Change Network) sun jinjina tare da yabawa shugaba Buhari bisa kokarin gwamnatinsa na yaki da cin hanci a Najeriya.

Jagorar kungiyar, Uwargida Josephine Okpara, ce tayi wannan yabo a madadin mambobin kungiyar, yayin gudanar da wani tattakin nuna goyon bayan Buhari a Legas.

Okpara ta bayyana cewar ko a yanzu kokarin shugaba Buhari na yaki da cin hanci ya biya kudin sabulu domin an yi nasarar kwato wasu daga cikin kudin kasar nan da jami’an gwamnati a baya suka sace.

Kungiyar mata ta gudanar da tattakin nuna goyon baya ga Buhari, sun caccaki Obasanjo

Kungiyar mata ta gudanar da tattakin nuna goyon baya ga Buhari

Kazalika, Okpara, ta ja kunnen tsohon shugaban kasa Obasanjo da ya guji sukar gwamnatin Buhari a kokarin da take yin a tsamo Najeriya daga matsalar da mulkinsa da wasu shugabannin baya suka jefa kasar a ciki.

DUBA WANNAN: Jihar Akwa Ibom tayi cikar ban mamaki yayin bikin karbar Akpabio zuwa APC

Muna kira ga shugaba Buhari da ya mayar da hankali wajen cigaba da aiyukan alheri da yake yi a Najeriya. Kada ya damu da zancen masu adawa da basa kaunar Najeriya, mutanen da suka amfanar da kasa komai lokacin da suke da dama,” a cewar Okpara.

Okpara ta mika godiyar tag a ‘ya’yan kungiyarsu bisa samun dammar halartar taron da suka yi jaddada goyon bayan su ga shugaba Buhari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel