Hadiman Ganduje na cigaba da barin Gwamnatin Jihar Kano

Hadiman Ganduje na cigaba da barin Gwamnatin Jihar Kano

Mun samu labari cewa Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya sake rasa wata babba a cikin Gwamnatin sa. Wata mai ba Gwamnan Jihar shawara ce tayi murabus ta ajiye aikin ta a cikin makon nan.

Hadiman Ganduje na cigaba da barin Gwamnatin Jihar Kano

Mai Girma Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya rasa Hadimai 10

Rukayya Jibrin wanda ta ke ba Mai Girma Gwamna Abdullahi Ganduje shawara wajen sh’anin yaki da shan miyagun kwayoyi a Kano ta bar kujerar ta. Jibrin tace ya zama dole ta bar ofis bayan Mataimakin Gwamnan Jihar ya ajiye aikin sa.

Wannan Baiwar Allah tace ba za ta cigaba da aiki a Gwamnatin ba bayan Mai Gidan ta Farfesa Hafizu Abubakar yayi murabus. Mataimakin Gwamnan ya ajiye aiki ne a karshen wancan makon bayan ya samu sabani da Gwamna Ganduje.

KU KARANTA: Wasu manyan kusoshin PDP za su koma APC a Kudancin Najeriya

Tuni dai har Sakataren Gwamnatin Jihar Kano yayi na’am da takardar Rukaya Jibrin wanda tayi wa Gwamnan Jihar godiya na ba ta wannan dama. Hadiman Gwamna Ganduje kusan 6 kenan mu ka samu labari sun yi murabus a makon nan.

Kafin nan dama wani Hadimin Gwamnatin Jihar Hafizu Dahiru Alkali ya ajiye aikin sa bayan da Hafizu Abubakar ya bar kujeran Mataimakin Gwamna. Alhaji Hafizu Dahiru Alkali yace ba zai iya hakuri da wulakancin da ake yi masu ba.

Ku na da labari cewa Gwamna Abdullahi Ganduje ya aikawa tsohon Mataimakin sa Farfesa Hafiz Abubakar takarda inda ya amince da matakin da ya dauka na barin ofis. Gwamnan ya nemi Hafiz Abubakar ya koma Jami’a inda ya fi wayau.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel