Gwamnatoci a Najeriya basu iya jure wa adawar siyasa - Bukola Saraki

Gwamnatoci a Najeriya basu iya jure wa adawar siyasa - Bukola Saraki

- Gwamnatin Najeriya ta kasa zaune, ta kasa tsaye saboda jam'iyyar adawa

- Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya sauke shugaban yan sandan farin kaya, Lawal Daura

- A tunani na da muka bukaci canji, bamu taba tsammanin irin wannan canjin ba, inji Saraki

Gwamnatoci a Najeriya basu iya jure wa adawar siyasa - Bukola Saraki

Gwamnatoci a Najeriya basu iya jure wa adawar siyasa - Bukola Saraki
Source: Depositphotos

A yau ne shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya zargi Gwamnatin Najeriya da rashin jure wa adawa. A jiya ne jami'an tsaro na farin kaya suka hana mahukuntan shiga zauren majalisar.

Jami'an sunce suna aiki ne akan "Doka daga sama". Amma gwamnatin Najeriya ta musa akan ba ita tasa su ba.

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, wanda ke aiki a matsayin shugaban kasa Muhammadu Buhari da a yanzu yake hutun kwana goma a UK, ya sauke shugaban yan sandan fararen kaya, Lawal Daura kuma ya maye gurbin shi da Mathew Seivafa.

Dole ince, lokacin da mukayi ta fafutukar neman canji, bamu San irin wannan abinda ya faru jiya zai faru ba - yanayin da mutane basu iya jure bambancin ra'ayoyi domin cigaban kasar mu, inji Saraki, a taron manema labarai daya hada na yau laraba.

Saraki da ya dandani makamancin hakan a sati uku da suka gabata, inda yan sanda suka zagaye gidanshi da ke Abuja, suka kuma tabbatar da cewa gwamnati ce tasa su.

Ya kuma jinjiinawa mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da ya sauke Daura, wanda hakan yasa jami'an tsaron suka bar majalisar. Yace abinda Osinbajo yayi ya dawo musu da tabbacin su.

DUBA WANNAN: Farashin mai ya kusa dala $76

Amma duk da haka, shugaban majalisar yace hukuncin bai shawo kan matsalar ba tunda ba a san ta yadda tushen al'amarin yake ba.

Jam'iyyar APC mai mulki tace zuwan yan sandan farin kaya don kawai su hana tashin hankali ne.

Jam'iyyar APC tace bincike ya nuna cewa da sa hannun shugaban majalisar a zuwan jami'an. Ta kuma zargi shugaban majalisar wanda a karshen watan jiya ya canza sheka zuwa PDP da laifin kawo tsageru don su hana tsige shi daga kujerar shi. Inji mai magana da yawun jam'iyyar APC Yekini Nabena

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel