Yanzu Yanzu: Saraki na cikin ganawar sirri da IBB a Minna

Yanzu Yanzu: Saraki na cikin ganawar sirri da IBB a Minna

Bayan mamaya da jami’an yan sandan farin kaya, DSS suka kai majalisar dokokin kasar wadda ya haifar da cece-kuce a ranar Talata, shugaban majalisar dattawan Bukola Saraki na cikin ganawar sirri da tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida.

Shugabannin guda biyu sun shiga ganawar ne a gidan tsohon shugaban kasar dake garin Minna, babban birnin jihar Niger.

Yanzu Yanzu: Saraki na cikin ganawar sirri da IBB a Minna

Yanzu Yanzu: Saraki na cikin ganawar sirri da IBB a Minna

A lokacin wannan rahoto babu cikakken bayani akan dalilin ganawar tasu, sai dai majiyoyi sun nuna cewa babu mamaki Saraki ya tuntube shi ne don jin menene mafita.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Sanata Jonah Jang na neman kujerar shugabancin kasa a zaben 2019

Idan dai bazaku manta ba a jiya ne mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya salami shugaban hukumar DSS Lawal Daura akan mamayar da jami’ansa suka kai majalisar dokokin kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel