Yanzu Yanzu: Sanata Jonah Jang na neman kujerar shugabancin kasa a zaben 2019

Yanzu Yanzu: Sanata Jonah Jang na neman kujerar shugabancin kasa a zaben 2019

Tsohon gwamnan jihar Plateau kuma sanata mai ci a yanzu, Jonah David Jang ya bayyana kudirin san a tsayawa takarar shugabancin kasa a zaben 2019 mai zuwa karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP.

Sanata Jang wanda ya kasance mutun na farko da nuna ra’ayinsa akan kujerar daga yankin arewa ta tsakiya yace kudirinsa ya samo asali ne daga kokarinsa na son ganin yayiwa Najeriya aiki.

Yanzu Yanzu: Sanata Jonah Jang na neman kujerar shugabancin kasa a zaben 2019

Yanzu Yanzu: Sanata Jonah Jang na neman kujerar shugabancin kasa a zaben 2019

Yace zai yi kokarin kawo hadin kai da zaman lafiya idan har aka bashi dama.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Shugabannin majalisar dokokin kasar sun gana da shugaban INEC

Jang yayi alkawarin cewa ba zai ba mutanen Najeriya kunya ba idan har aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel