Da duminsa: Kasa da sa’o’i 24 da rufe asusun jihar Benuwe, EFCC ta kara rufe asusun wata jihar kudu

Da duminsa: Kasa da sa’o’i 24 da rufe asusun jihar Benuwe, EFCC ta kara rufe asusun wata jihar kudu

Hukumar yaki da cin hanci da yiwa tattalin arziki ta’annati (EFCC) ta rufe asusun ajiyar kudin gwamnatin jihar Akwa Ibom.

Wani babban jami’in gwamnatin jihar ta Akwa Ibom ne ya tabbatar wa da jaridar The Cable faruwar hakan.

Majiyar ta shaidawa The Cable cewar gwamna Udom Emmanuel na jihar Akwa Ibom da babban akawun jihar sun nuna matukar kaduwa da wannan mataki na hukumar EFCC.

Da duminsa: Kasa da sa’o’i 24 da rufe asusun jihar Benuwe, EFCC ta kara rufe asusun wata jihar kudu

Jami'an EFCC

Labarin rufe asusun jihar ta Akwa Ibom na zuwa ne cikin kasa da sa’o’i 24 da hukumar ta EFCC ta rufe asusun jihar Benuwe.

DUBA WANNAN: Hotuna daga bikin karbar Akpabio zuwa jam'iyyar APC

Kakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, bai samu dammar amsa bukatar jaridar ta The cable na tabbatar da labarin ba balle ya sanar da ita dalilin daukan wannan mataki.

Zamu kawo maku Karin bayani….

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel