APC tayi amai ta lashe ta goyi bayan hana sanatoci shiga majalisa

APC tayi amai ta lashe ta goyi bayan hana sanatoci shiga majalisa

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta goyi bayan matakin da jami'an tsaron farin kaya (DSS) suka dauka ranar Talata na hana sanatoci shiga majalisar dattawan kasar.

Wata sanarwar da mukaddashin kakakin jam'iyyar, Yekini Nabena, ya fitar ta ce binciken da jam'iyyar ta gudanar ya gano cewa shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ne ya shirya tayar da zaune tsaye domin hana yunkurin tsige shi.

Ta kuma ce da ba don jami'an tsaro ba, da an yi tashin hankali da ka iya haddasa salwantar rayuka a majalisar.

APC tayi amai ta lashe ta goyi bayan hana sanatoci shiga majalisa

APC tayi amai ta lashe ta goyi bayan hana sanatoci shiga majalisa

Ta ce Saraki ya kai 'yan bangar siyasa majalisar kuma saura kiris 'yan bangar su kashe dan majalisar wakilai na APC daya tilo da ya je majalisar, E.J. Agbonayinma, da ba don taimakon jami'an tsaro ba.

Jam'iyyar ta kuma nemi sanin dalilin da ya sa shugaban majalisar dattawa ya kira taron 'yan majalisa domin dakile yunkurin wasu 'yan majalisa na tsige shi.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da takwaransa na majalisar wakilai Yakubu Dogara sun bayyana cewa rashin zaman majalisar da bai samu ba a jiya ya ta'allaka ne akan yadda jami'an rundunar tsaro ta farin kaya suka yiwa majalisar tsinke, tare da hana mambobin majalisar shiga zauren majalisar domin tattaunawa.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Shugabannin majalisar dokokin kasar sun gana da shugaban INEC

Tun da farko dai shugaban majalisar dattawan Bukola Saraki ya kirawo zaman majalisar na gaggawar domin sake yin nazari akan kasafin kudin da hukumar zabe ta kasa wato INEC ta bukata, kamar yadda shugaba Muhammad Buhari ya bukace su da su zauna.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel