Da dumi-dumi: Shugabannin majalisar dokokin kasar sun gana da shugaban INEC

Da dumi-dumi: Shugabannin majalisar dokokin kasar sun gana da shugaban INEC

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara sun gana da shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Mahmood Yakubu a Abuja.

Sun yi ganawar ne domin tattauna batun kudin zaben 2019 da kuma gyara dokar zabe.

Shugaban majalisar dattawa a ranar Litinin ya shirya wata ganawa da shugaban INEC wadda ya kamata ace anyi a jiya Talata amma aka daga saboda mamayar da jami’an DSS suka kai majalisar dokokin kasar.

Da dumi-dumi: Shugabannin majalisar dokokin kasar sun gana da shugaban INEC

Da dumi-dumi: Shugabannin majalisar dokokin kasar sun gana da shugaban INEC

Saraki a ganawarsu ta yau ya nemi sanin dalilin da yasa aka gabatar da bukatar kudi ga majalisar dokoki kusan makonni uku ba wai watanni ba.

Ya bayyana cewa majalisar dokoki ta jajirce domin ganin cewa a gabatar da zabe ba tare da matsaloli ba.

KU KARANTA KUMA: Hukumar EFCC ta daskarar da asusun gwamnatin Benue a bankuna 3

Shugaban majalisar dattawan ya kuma roki shugaban kasar da ya sanya hannu a gyara dokar zabe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel